1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan Human Rights Watch akan Kenya

Shuaibu Othman Sambo March 18, 2008

Ƙungiyar kare hakkin jama'a ta ƙasa da kasa ta bukaci gudanar da binciken tushen rikicin Kenya

Babban Directan Human Rights Watch,Jose Miguel Vivanco.Hoto: AP

Ƙungiyar fafutukan 'yancin bil Adama ta ƙasar Amurka ta Human Right Watch(HRW) ta ƙalubalanci sabuwar Gwamnatin haɗaka ta ƙasar kenya da ta gaggauta gano mafita ko kuma sulhu ga rikicin ƙasar domin kaucewa sakewar bullar tashe tashen hankulan da suka faru a bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka yi watan Disambar bara.

Cikin wani rahoto mai shafi 81,da ƙungiyar ta fitar wanda kuma ta yi wa taken "ƙaluballen tashin hankali bayan zaɓe watan Disamba a ƙasar kenya", ta bayyana cewa har sai mambobin sabuwar gwamnatin haɗakan da aka samar a kenya bayan cimma yarjejeniyar sulhu ta hanzarta kafa wasu sababbin hukumomi da za su yi aiki da gaskiya wajen gudanar da bincike kan sabunta dokokin zaɓen a ƙasar da kuma hukunta dukkan waɗanda a ka gano na da hannu wajen tunzura rikici da ya afku a ƙasar bayan faɗar sakamakon zaɓe a ranar 17 ga Disamban2007, kafin a tabbatar da ingancin sabuwar gwamnatin .

Mr Tom Porteous Wani darakta a ofishin hukuma HRW ɗin da ke birnin London ga kuma Karin bayanin da ya yi min don gane da binciken da kuma nazarin tushen rikicin kenya da hukumar ta gabatar..

"Daga cikin abin da muka gano a binciken da muka gudanar bayan kammala zaɓe a kenya shi ne wannan rikici da ya faru na musamman ne domin kuwa shugabannin ƙabilu da masu hannu da shuni da kuma shugabannin jam'iyyun adawa waɗanda ke neman suna ko kuma matsayi, sune su ka ƙuƙƙulla shi .kuma a ra'ayimmu muna gani idan har ana son kaucewa sake afkuwar irin wannan rikici a nan gaba to ya kamata a gudanar da kyakkyawan bincike domin hukunta duk wanda aka gano yana da hannu a ciki."

Haka kuma rahoton ya bayyana cewa jami'an tsaro sun taka rawa wajen ingiza rikicin, ta hanyar yin anfani da ƙarfin da ya wuce misali da kuma bindigogi wajen hana zanga-zanga tare da hallaka ɗaruruwan masu zanga-zanga da 'yan kallo.Inda mr Tom ya ce;

"Sunyi anfani da tsauraran matakai da suka haɗa da kashe-kashe na ba dalili,nan ma muna ganin cewa ya kamata a gudanar da bincike wanda haka ne zai tabbatar da irin kudirin da sabuwar gwamnatin ke da shi na aiwatar da gaskiya.

A danmgane da ko su wa da waye za a hukunta ganin cewa mafiya yawa daga cikin waɗanda ake zargi da iza wutar rikicin bayan zaɓen sune a cikin gwamnatin gambizar;sai ya ce

"Haƙiƙa wasu daga cikin waɗanda suka yi kulle-kullen da ta kai ga rikicin suna cikin gwamnati.To Abu mai mahimmanci anan shi ne idan aka zo binciken da za a gudanar game da sanadiyyar tashin-tashinar da ta afku a ƙasar Kenya sai a yi shi ba tare da son zuciya ba ko banbanci ta yadda duk wanda aka samu da laifi komai matsayinsa sai ya fuskanci shari'a.

A watan da ya gabata ne dai shugaba Mwai Kibaki na Kasar ta Keny tare da madugun 'yan Adawa Raila Odinga suka amince da kafa sabuwar gwamnatin gambiza da za ta ƙunshi wakilai daga dukkan sassan da basa ga maciji da juna a ƙasar.Bayan kwashe sama da watanni biyu ana bata kashi a kenya bayan sanar da sakamakon zaɓen ƙasar.Lamarin da ya hallaka sama da mutane dubu kana wasu fiye da dubu 500 kuma suka rasa matsugunensu.