1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin sojin Kamaru ya dauki hanaklin jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
July 21, 2017

Wasu jaridun Jamus sun dubi rahoton da kungiyar Amnesty International inda ta zargi sojojin kasar Kamaru da cin zarafin mutanen da ta kama bisa zargin kasancewa 'yan kungiyar Boko Haram.

Deutschland PK Amnesty International Report 2016/2017
Hoto: DW/N. Jolkver

Jaridar ta ce hotuna da bayanan da shaidu suka bayar na zama shaida kwakkwara da Amnesty International ta ce na cin zarafin dan Adam a cikin rahotonta mai taken "Sansanonin azaba na sirri na kamaru". A hotunan ana iya ganin sojojin Amirka a sansanin sojin Kamaru na Salak da ke arewacin kasar, inda ake aka yi ta gana wa 'yan kungiyar Boko Haram azaba. Shaidu dai sun tabbatar cewa sun ga fararen fatu a sansanin lamarin da daraktan bincike na Amnesty International a yankin yammaci da tsakiyar Afirka, Stephen Cockburn ya ce ba wanda ya dauki matakin dakatar da cin zarafin wadanda ake zargin. Ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu sojojin Amirka na da masaniya a kan batun, a saboda haka ya yi kira da a dauki matakan da suka dace.

Siyasar Afirka ta Kudu

Hoto: Reuters

A Afirka ta Kudu kawancen jam'iyyu uku mai cike da tarihi ya kusa rushewa bayan babban taron jam'iyyar SACP, inji jaridar Neues Deutschland. Jaridar ta ce jam'iyyar SACP ta masu ra'ayin Kwaminis ta kawo karshen babban taronta karo na 14 da nuna goyon bayan janye daga kawance, inda za ta yi gaban kanta a zabe mai zuwa. Jaridar ta ce hakan na nufin ke nan a watan Disamba mai zuwa za a kawo karshen kawancen jam'iyyu uku da suka hada da ANC da SACP kanta da kuma COSATU ta 'yan kungiyoyin kwadago. A cikin watan Disamban ne ANC za ta zabi sabon shugaban jam'iyya da zai tsaya mata takara a zaben 2019. Kasancewa Shugaba Jacob Zuma ba zai iya sake tsayawa takara ba bayan wa'adin mulki na biyu, ya tsaya kai da fata sai a zabi tsohuwar matarsa Nkosazana Dlamini-Zuma a wannan mukami, abin da bai yi wa jam'iyyar SACP dadi ba.

Matsalolin 'yan gudun hijira a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango

Hoto: DW

A karshe sai kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango inda jaridar Die Tageszeitung ta buga labari mai taken "Ba abinci ba ruwa ba tufafi", tana mai cewa; yanzu haka akwai 'yan gudun hijira na cikin gida kimanin miliyan 3.8 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, kuma a kullum halin da suke ciki na kara yin muni. Ta ce yayin da a hannu daya yawansu ke karuwa babu kakkautawa, a daya hannun kuwa taimakon da suke samu ya ragu matuka. Yankin Kasai mai fama da rikici ke kan gaba na yawan 'yan gudun hijira inda aka tilatsa wa miliyan 1.4 barin gidajensu a dalilin fadan da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da mayakan sakai na 'yan adawa. Larduna 15 daga cikin 26 na Kwango na fama da kwararar 'yan gudun hijira na cikin gida.