1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon rahoton ENDSARS ya bar baya da kura

November 16, 2021

Kwamitin da gwamnatin jahar Legas ta kafa don gudanar da bincike kan rikicin ENDSARS yayi bayani kan yawan kudaden da aka bayar a matsayin diyya ga wadanda suka tafka asarar rayuka da dukiya.

Nigeria Lagos | EndSars Demonstration
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

A jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya kwamitin da gwamnati ta kafa kan zanga-zangar EndSars da ake zargin jami'an tsaro da wuce gona da iri ya gabatar da rahotonsa inda a ciki, aka nemi a biya diyya na kimanin Naira miliyan 410, ga mutane 70 da rikicin ya shafa.

A daya bangaren kuwa, Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, batun kisan masu zanga-zangar ta #EndSARS na kunshe cikin rahoton bincike da aka mikawa gwamnatin jahar Legas. Duk da cewa ba a fitar da rahoton ga jama'a ba, amma kamfanin dillancin labaran na Reuters ya ce masu binciken sun siffanta abin da sojojin suka yi a shekarar da ta gabata a matsayin kisan gilla da sunan tarwatsa masu zanga-zangar ta #EndSARS da masu fafutuka suka shirya a kan zargin cin zarafi da jami'an 'yan sandan rundunar SARS ke yi a kasar.

An zargi jami'an tsaro da amfani da karfi kan masu zanga-zangaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Kawo yanzu dai hukumar soja da ta 'yan sandan kasar ba su ce uffan ba kan wannan sabon rahoton, sai dai a baya sun sha nanata cewa ba su yi amfani da harsashi mai rai ba kan masu zanga-zanga. To amma masu rahoton sun ce sun ga alamun 'yan sanda sun yi kokarin boye wasu hujjojin irin tabargazar da jami'an tsaro suka yi a Lekki Toll Gate da ke Lagos inda aka yi wannan artabu.

Jami'an rundunar sojojin Najeriya sun yi amfani da harsashi mai rai, yayin tarwatsa masu zanga-zangar #EndSARS a jahar Legas cikin shekarar da ta gabata ta 2020.