1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton hukumar kare hakin bil adama ta Human Right Wacth akan Siriya

December 15, 2011

Hukumar ta ce sojojin ƙasar Siriya sun aikata kisan gila akan fararan hula, bayan wani binciken da ta yi inda ta yi tambayoyi ga wasu sojojin da suka canza sheƙa

Pro-Syrian regime protesters, shout pro-Syrian President Bashar Assad slogans during a demonstration in Damascus, Syria, on Wednesday Nov. 16, 2011, during a demonstration against the Arab League meeting being held in Morocco. The Arab League is expected to formalize its weekend decision to suspend Syria from the Arab League, for failing to end its crackdown against anti-government protesters.(Foto:Muzaffar Salman/AP/dapd)
Masu zanga zanga a SiriyaHoto: dapd

Hukumar kare hakin bil adama ta Human Rights Wacth ta baiyana wani rahoton wanda a cikin sa ta ke zargin sojojin ƙasar Siriya da laifin aikata kisan gila akan farara fula.Hukumar wacce ta ce ta tattauna da sojojin gwamnatin Bashar Al Assad wanɗada suka arce suka canza sheƙa domin bin bayan sahun masu gudanar da zanga zangar ta ce sun shaidama ta yadda aka aikata kisan.

Wani sojojin gwamnatin ƙasar Siriyan da ya amsa tambayoyin hukumar ta kare hakin bil adama ya baiyana halin da ya samu kansa a ciki ''ya ce masu harbin ɗauki ɗaya ɗaya guda biyu ke bani umarnin kafin hawa kan gine gine inda da gana muke yin harbi kan masu zanga zanga.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman