1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton shekara na Amnisty International

May 23, 2006

Hukumar kare haƙƙoƙin bani adama ta dunia, wato Amnisty International, ta bayana rahoton ta na shekara , a game da halin yancin jama´a shekara ta 2005.

Wannan rahoto ya ce, a sassa daban daban na dunia, a wannan shekara ta 2005, an ci gaba da take haƙƙoƙin jama´a, to saidai, duk da haka, an ɗan samu ci gaba, idan a kwatanta da shekarun da su ka gabata.

Hukumar ta yi zargi da kakaussar halshe, ga ƙasashen China, Rasha, Sudan da Colombia, wanda a nan ne hukumomi ke gana uƙuba ga jama´a.

Sannan rahoto, ya bayana Amurika da Britania, da wasu yan amshin shatan su, a matsayin ƙasashen da ke fakewa bayan yaƙi da ta´adanci, domin ƙuntatawa mutane.

Amnisty ,ta yi suka ga gidan gwalegwalen Gwantanamo, na ƙasar Cuba, inda Amurika ke cigaba da tsare mutanen da ta ke zargi, da aikata ta´adanci.

A game da nahiyar mu ta Afrika,

rahoton Amnisty, ya ce ƙasashen yankin Magreb, sun shahara ta fannin, kulle masu adawa da manufofin gwamnati, da kuma hana yan jarida faɗin albarkacin bakin su.