1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

rahoton UNICEF

September 30, 2005

Kasashen yammaci da na tsakiyar Afurka na fama da mace-macen yara

Rahoton UNICEF
Rahoton UNICEFHoto: AP/UNICEF
Matsalar ta mace-machen yaran da ba su kai shekaru biyar na haifuwa ba ta fi shafar yankunan yammaci da tsakiyar Afurka, musamman a kasashen da ake fama da rikice-rikice a cikinsu, kazalika har da Nijeriya, in ji kungiyar ta UNICEF. A yayinda a cikin shekarun 1980 aka samu kyakkyawan ci gaba a matakan lambar riga kafi ga kananan yara a sassa daban-daban na duniya, lamarin ya samu koma baya a shekarun 1990, a wani bangaren kuwa, sakamakon raguwar yawan taimako ga kasashe masu tasowa da kuma tabarbarewar tattalin arzikinsu. Dr. Peter Salama, shugaban sashen lambar riga kafi na kungiyar UNICEF ya fada a wani taron manema labarai cewar a wancan lokaci an yi zaton cewar ci gaban da ake samu zai dore, amma sai ga shi daga baya murna ta koma ciki. Kimanin yara miliyan 30 ake haifuwarsu a kowace shekara tun abin da ya kama daga shekarar 1990 kuma akwai wasu kasashe 103 dake bakin kokarinsu wajen kare makomar rayuwar kashi 90 cikin dari na yaran da a kann haifa ta hanyar lambar riga kafin wasu cututtukan da ba su gagari magani ba. A dai halin da ake ciki yanzu kimanin dala miliyan dubu daya ake kashewa akan lambar riga kafi ga kananan yara kuma ana bukatar karin wasu dalar Amurka miliyan dubu daya domin matakin ya zama na gama gari daidai da manufar Majalisar dinkin Duniya game da yi wa kashi 90 cikin dari na yara lambar riga kafi nan da shekara ta 2010. To sai dai kuma wannan adadi na kudi mai yiwuwa ya karu zuwa dala miliyan dubu shida sakamakon riga kafin wasu cutukkan dabam, kamar dai cutar gudawa. Wasu alkaluman da aka bayar sun nuna cewar a yanzu kimanin yara miliyan biyu, ‚yan kasa da shekaru biyar ake kare makomar rayuwarsu sakamakon lambar riga kafi a duk shekara. A lokacin da take bayani wata jami’ar kungiyar ta UNICEF ta ce wajibi ne a kare makomar ci gaban da ake samu a kuma fadada matakin zuwa sauran bangarori. A cikin rahoton nata kungiyar UNICEF ta ce a yayinda a yankunan Latin Amurka da Karibiya da kuma Gabas ta tsakiya ake wa kashi 90 cikin dari na yaran da ake haifa lambar riga kafi, an samu koma baya zuwa kashi 88 cikin dari a yankunan tsakiya da kuma gabacin Turai tsakanin 1988 zuwa shekara ta 2001. A yankin kudancin Asiya adadin ya kama kashi 71 a yayinda a yankunan yammaci da kuma tsakiyar afurka adadin ya kama kashi 48 cikin dari kacal. Amma abin mamaki kasa kamar Eritrea wadda ta sha fama da yaki ta samu kyakkyawan ci gaba daga kashi 18 a shekara ta 1990 zuwa kashi 84 cikin dari a shekara ta 2003. Su ma kasashe masu ci gaban masana’antu suna fama da koma baya ko da yake ba sa fuskantar mace-machen yaran sakamakon wadataccen abinci mai gina jiki da suke da shi