1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton WHO a game da cuttutuka a ƙasar Sudan

Yahouza SadissouMarch 31, 2006

WHO ta bayyana rahoto a game da ɓarkewar cutar kwalara da sanƙarau a ƙasar Sudan

Hoto: AP

Wannan rahoto da WHO, kokuma OMS ta bayyana, a yau juma´a ,ya ce miliyoyin mutane ne, a ƙasar Sudan, ke fama da cuttutuka, iri iri,da su ka haɗa da Cholera da sanƙarau.

A ko wace rana, mutane da dama, ke kamuwa da wannan cututuka 2, jama´a da dama na rasa rayuka.

A halin da a ke ciki,al´ammarin na da matuƙar tada hankali inji, Ala Din Alwan, kakakin hukumar majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da harakokin kiwon lahia.

WHO, na bukatar dalla milion 24, domin samara da magani na tallafi ga jama´ar wannannkasa, mussaman, a yankunan da cuttutukan su ka fi ƙamari.

Kazalika, a watani 6, da su ka gabata,ƙasar Sudan, ta yi fama da wasu ƙarin cuwarwata, kamar su gudawa, shawara, tari, da kuma sauran wasu malati, da su ka jaɓanci anfani da ruwa gurbattatau.

Bincike ya gano cewra mutane, million ɗaya da rabi, su ka kamu, da cuta Sankarau, a jihohi 15, daga jimilar jihohi 25 na ƙasar.

A halin da ake ciki,Cutar na ci gaba da bazuwa bazuwa,kamar wutar daji, a dalilin ƙarancin magani da rashin mattakan tsabta, da kuma yawan cuɗayya tsakanin al´umma.

Idan ba ayi komi a kai ba, cikin gaggawa, to al´ammari zai iya zama gagarabadau.

Rahoton na Hukumar WHO ya ce, a dangane da cutar gudawa, mutane kussan dubu 10, su ka kamu da ita, a cikin jihohi 7, na kudancin ƙasar.

Mutane 248 daga cikin su, sun riga mu gidan gaskiya.

WHO, ta yi kira ga ƙasashe masu hannu da shuni, da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa da su gaggauta kai taimakon ga al´umomin kasar Sudan.

Saidai abun damuwa imnji rahoton shine a yanzu haka kungiyoyin bada agaji da ke aiki a ƙasar, na kokawa, da rashin issasun mattakan tsaro, a dalili da rikicin da ke ci gaba da wanzuwa, tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnati.

Saboda haha, hukumar OMS, ta yi kira ga gwamnati, da ya tawayen Darfur, da su bada haɗin kai, ga wannan ƙungiyoyi, domin ta haka kawai, za a iya samar da nasara ceton rayukan jama´a.