1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya: Odinga ya kalubalanci sakamakon zabe

Suleiman Babayo ZMA
August 22, 2022

Jagoran ''yan adawa na Kenya Raila Odinga ya kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zabe ta sanar saboda sabanin da ke tsakanin allaluman.

Kenia | Raila Odinga
Hoto: Thomas Mukoya/REUTERS

Jagoran 'yan adawa na kasar Kenya, Raila Odinga ya shigar da koke gaban kotun kolin kasar inda ya kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 9 ga wannan wata na Agusta, da hukumar zabe ta sanar da mataimakin shugaban kasar William Ruto a matsayin wanda ya yi nasara.

Odinga mai shekaru 77 da haihuwa ya shigar da koken gabanin wa'adin da aka gindaya na tabbatar da shigar da kara kar ya wuce mako guda bayan sanar da sakamakon zaben. Magoya bayan jagoran 'yan adawa sun hallara a kotun kolin lokacin shigar da koken. Odinga ya nemi kotun ta soke sakamakon zaben saboda sabanin da ke tsakanin alkaluman da yadda hukumar zaben ta gaza nuna kuri'un wasu mazabu na gundumomi 27 kamar yadda dokokin kasar suka tanada.

Lokacin yakin neman zaben jagoran 'yan adawa Raila Odinga ya samun goyon bayan Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar ta Kenya.