1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin fitowar jama'a wajen karbar katunan zabe a Kano

Nasir Salisu Zango AH
September 2, 2025

Yayin da aka fara aikin yin sabbin katunan zabe da gyara ga masu bukata a fadin Najeriya. Jihar Kano jiha mafi yawan jama'a a fadin kasar ta zama kurar baya na yawan wadanda suka fara karbar katunan.

Tsohon hoto na zabe a Najeriya
Tsohon hoto na zabe a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Kawo yanzu dai mutanen da suka fara karbar katunan zaben a Jihar Kano ba su kai sun kawo ba idan aka kwatanta da Jihohin irin  Lagos da Rivers da sauran su, wannan mataki dai ya daga hankalin mahukunta a Jihar Kano wadanda suka tashi haikan domin ganin cewar a dauki matakan cike wannan gibi, Alkali Sunusi Abdullahi magidanci ne me fashin baki kan lamuran yau da kullum a Kano ya ce dole sai an tashi tsaye.

Gwamnatin Kano dai ta damu kwarai da samun wadannan alkalluma har ma kuma ta dauki matakan tabbatar da wayar da kan jama'a  a kan gane muhimmancin karbar katunan zaben, Comrade Abdullahi shi ne kwamishinan yada labarai na Jihar Kano kuma shugaban babban kwamitin wayar da kan jama'a a kan karbar katin zaben ya yi bayanin matakan da ake dauka domin cike wannan gibi:

Tsohon hoton zabe a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

''Yanzu haka dai hukumar zabe ta kasa ta ce ta samar da yanayi me kyau da zai bai wa kowa damar yin  rajista ko gyarawa cikin sauki domin an yi tanadi na musamman ga masu bukata ta musamman haka kuma akwai damar yin tsarin tafi da gidan ka ta hanyar yin rajista a duk in da mutum yake ta hanyar intanet,

Nahila Bello Dandago ita ce mai magana da yawun hukumar INEC a Kano ta bayyana cewar su dai a nasu bangaren sun yin tanadin tabbatar da cewar ba a bar kowa a baya ba:

''Ana yin rajistar ne dai domin bayar da dama ga matasa da suka shiga shekara 18 da haihuwa a bana, da kuma bayar da gyara ga wadanda ko dai suka batar da tasu rajistar ko kuma suke da wata matsala da suke son gayarawa.''

Tsohon hoton zabe a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Sai dai rashin fitowar jama'ar  kano ya   tasamma zama wata babbar barazana da ke daga hannkalin mahukunta wadanda suka soma kaddamar da aikin fadikar da jama'a a mahimmancin katin zaben.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani