1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ramaphosa shi ne sabon shugaban jam'iyyar ANC

December 18, 2017

Wakilan jam'iyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu sun zabi mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugaban jam'iyar da zai gaji  Shugaba Jacob Zuma da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Südafrika ANC Parteitag Ramaphosa
Hoto: Getty Images/AFP/G. Khan

Kimanin wakilan jam'iyar dubu hudu da dari bakwai ne suka kada kuri'a wajan zaben sabon shugaban jam'iyar ta ANC a wani a zabe da aka yi ta jan kafa kafin soma kada kuri'a, da ma sanar da sakamonshi. 'Yan takarar da suka fafata a zaben dai su ne Cyril Ramaphosa mataimakin shugaban kasar da kuma Nkosazana Dlamini Zuma tsohuwar mata ga Shugaba Jocob Zuma.

Mataimakin shugaban kasar yayi nasara ne da kuri'u 2440 a kan abokiyar karawar shi wacce ta samu kuri'u dubu biyu da dari biyu da sittin da daya.

Rabuwar kai ta bayyana a jam'iyyar ta ANCHoto: Getty Images/AFP/M. Safodien

Dama dai tun kafin tafiya ta yi nisa a kafara ganin alamun mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa zai yi nasara a zaben ganin cewa Nkosazana Dlamini ka iya dorawa ne daga inda tsohon maigidanta zai tsaya, abin da da yawa ke adawa da salon mulkin sa. Samododa Fikeni -wani mai sharhi ne kan al'amuran yau da kullum a kasar.

''Ta gaji tsarin siyasar tsohon mijinta ne kuma tayi shiru game da abubuwa da yawa da ke faruwa musamman a kamfanonin gwamanati, da kuma abun da yake faruwa cikin gwamanatin Jacob Zuma, duka wadannan sun bata salon tafiyarta.''

A jawabi bankwana shugaban kasar Jacob zuma ya yi kiran hadin kai tsakanin 'ya'yan jam'iyar ta ANC da kawunan 'ya'yanta suka rarrabu, inda jigajigan jam'iyar suka ja layi tsakanin masu mara baya ga Dlamini Zuma da ta jagoranci hukumar hada kan Afirka ta AU da kuma Cyril Ramaphosa matamakin shugaban kasar.