1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ramaphosa ya fuskanci tambayoyi a majalisa

Binta Aliyu Zurmi
August 27, 2020

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya fuskanci tambayoyi masu zafi daga 'yan majalisa dangane da wawure kudi da aka ware domin yaki da cutar Covid-19 a kasar.

Südafrika Präsident Ramaphosa
Hoto: AFP

Wannan ne karon farko na jerin tambayoyi da shugaba Ramaphosa ya fuskanta a gaban 'yan majalisa tun bayan da ake ta rade-raden cin hanci da rashawa tsakanin manyan jami'an gwamnatinsa da ma wasu mambobin jami'iyyarsa. 


Ramaphosa ya yi alkawarin zurfafa bincike da ma kawo gyara a fannin da ke da alhakin kula da bangaren sayen kayayyakin yaki da cutar ta covid-19.

Kasar Afirka ta Kudu na zama kasa ta biyar a jerin kasashen duniya da annobar coronavirus ta addabe su, sai dai shugaban ya ce cin hanci da rashawa na taka muhimiyar rawa wajen yaki da cutar a kasar.