Afirka ta Kudu: Kalubalen Ramaphosa
May 25, 2019Talla
Sabon shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi rantsuwar kama aikin ne a gaban shugabannin gwamnatocin kasashen Afirka da dama. Bikin rantsuwar wanda ya gudana a Pretoria babban birnin kasar, an shirya 'yan sanda dubu 25 don tabbatar da tsaro.
A cewa Khusela Diko kakakin shugaban kasar, a lokacin kama rantsuwa Shugaba Cyril Ramaphosa zai tabo batun hadin kan kasa da samarwa matasa aikin yi da kuma farfado da martabar kasar a matsayin wacce ke fada a ji a harkokin nahiyar Afirka. Mai shekaru 66 a duniya, Ramaphosa ya kasance mataimakin shugaba Jacob Zuma tun a shekara ta 2014, sai dai akwai babban kalubale da ke jiransa musamman rashin aikin yi da kuma yakar cin hanci da rashawa.