1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me zai faru a ganawar Ramaphosa da Trump?

Abdul-raheem Hassan
May 21, 2025

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa zai gana da Shugaba Trump a daidai lokacin da kasashen biyu ke takun saka a kan sake tsugunar da ‘yan Afrika farar fata na Washington saboda zargin yi musu kisan kiyashi.

USA/Südafrika | Trump friert US-Hilfen für Südafrika ein
Shugaba Trump zai karbi bakuncin RamaphosaHoto: Ting Shen and Alfredo Zuniga/AFP

Ganawar shugabannin biyu a fadar White House na daukar hankali bayan da Shugaba Trump ya zargi gwamnatin Afirka ta Kudu da nuna wariyar launin fata ga Turawan kasar tare da zargin "kisan kare dangi" a kan tsirarun fararen fata manoma.

Fredson Guilengue na cibiyar nazarin harkokin diflomasiyya ta Rosa Luxemburg mai mazauni a birnin Johannesburg, ya ce ziyarar tana kunshe da sako mai karfi.

Me ya sa Amurka ta janye tallafin da take ba wa Afirka ta Kudu ?

'' 'Yan kasar Afirka ta Kudu na wasuwasin me zai faru a yayin ziyarar Shugaba Ramaphosa a Amurka." in ji Fredson Guilengue mai nazarin harkokin diflomasiyya ta cibiyar Rosa Luxemburg. Ya kara da cewa "La'akari da sanin halin Mr. Trump na zafafa kalamai ga abokan hamayyarsa, musamman yadda ya titseye Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a kwanakin baya."

Shugaba Ramaphosa, ya ce ganawar ce kadai hanyar wanke duk wani zargi tare da farfado da alakar kasashen biyu da ya fara ja da baya tun bayan kawo karshen tsarin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu a kasar a shekarar 1994.

Rikicin Gaza da kawance da China da yakin Ukraine da Rasha da batun kasuwanci na cikin abin da ya sa kasashen biyu suka raba garai "Duk da yadda Mr Trump ke fitar da Amurka daga yejeniyoyi da ma wasu hukumomi na duniya, to amma kungiyar G20 na da muhimmanci." A cewar Daniel Silke mai sharhi kan al'amuran yau da kullum.

Me ya sa Trump ke adawa da kasashen G20?

Wannan dai shi ne karon farko da Shugaba Donald Trump zai gana da wani shugaban nahiyar Afirka tun bayan dawowarsa mulki karo na biyu, Trump dai bai taba kai ziyara wata kasa ta Afirka ba a wa'adin mulkinsa na farko.

Ana sa ran cewa Shugaba Cyril Ramaphosa zai iya lallaba takwaran na sa na Amurka Donald Trump don halartar babban taron kungiyar G20 da za a gudanar a cikin watan Nuwamba mai zuwa a birnin Jonahannesburg, wanda tun asali ya nuna aniyarsa ta kin halarta.