Ranar babban zaben Amurka
November 5, 2024Dukkannin manyan 'yan takarar zaben Amurka, Donald Trump da kuma Kamala Harris sun yi ikrarin za su samu nasara a zaben yayin da suka kammala gangamin yakin neman zabensu a jihar Pennsylvania, da ke da yawan kuri'un da ke da tasiri a yawan wakilai na musamman da aka fi sani da Electoral College, da sauran manyan jihohin da suka fi tasiri a zaben.
Karin bayani: Harris da Trump na kace-nace a gangamin yakin neman zaben Amurka
Dukannin 'yan takarar biyu sun sake neman goyon bayan 'yan kasar da ba su kada zaben wuri ba, da su fito kwansu da kwarkwatarsu a yau. Tuni dai Tsohon shugaban kasar na jam'iyyar Republican, Donald Trump ya karkare yakin neman zabensa ne a Michigan inda zai koma gida, Florida domin ya kada kuri'arsa da kuma jiran sakamakon zaben mai jan hankali. Yayin da Kamala Haris ta jam'iyyar Democrat ta kammala yakin neman zabenta a jihar Philadelphia.