1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harshen uwa a kafofin sada zumunta

Gazali Abdou Tasawa SB/LMJ
February 21, 2023

Albakacin ranar harshen uwa ta duniya mun duba irin rawar da kafofin sada zumunta na zamani suke takawa wajen bunkasa harshe ko akasin haka a Jamhuriyar Nijar.

Afirka
Kafofin sada zumunta na zamaniHoto: ISAAC KASAMANI/AFP/Getty Images

A wannan Talata (21.02.2023) ake ranar harshen uwa ta duniya wacce hukumar ilimi da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta kaddamar 2000 domin raya harsunan da kuma tunkarar barazanar bacewar wasu harsunan a duniya da kuma nuna muhimmancin harsunan uwa wajen bunkasa ilimi da ci gaban kasashe. Albarkacin bikin na bana mun duba ci gaba ko akasi ga shafukan sada zumunta suka haifar ga Harshen Hausa a kasar ta Nijar.

Alkalumman dai sun nunar da cewa kimanin kaso 80 daga cikin 100 na 'yan Nijar na amfani ko kuma jin harshen Hausa wanda tun fil azal ya kasance harshen kasuwanci da ya hada kabilu da dama a Nijar din da ma wasu kasashen duniya. Sai dai kuma wasu na ganin tun bayan samuwar sabbin hanyoyin sadarwa na yanar gizo da shafukan sada zumunta na zamani, sun yi tasiri sosai wajen bunkasa harshen da yada shi a tsakanin kabilun kasar.

To sai dai wasu manazarta harshen na Hausa na ganin inda gizo ke saka a game da alakar shafukan sada zumunta da kuma harshen Hausa a Nijar shi ne wajen rubuta harshen.

Yanzu haka dai masu nazarin harshen na Hausa na gani idan har ba a dauki mataki ba to kuwa nan da ‘yan shekaru dabra da Hausar shafukan sada zumuntar za su haifar da wani sabon harshen creol na harsunan kasar ta Jamhuriyar Nijar cakude.