1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar nada shugaban rikon kwarya a Burkina

Mouhamadou Awal Balarabe
October 8, 2022

Sabon shugaban mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya sanar da 14 da 15 ga watan Oktoba a matsayin ranukan tattaunawa don nada shugaba da zai yi rikon kwarya har zuwan lokacin da za a gudanar da zabe a 2024.

Lage in Burkina Faso I 2. Oktober 2022
Hoto: Vincent Bado/REUTERS

 Wata doka da aka karanta a gidan talbijin na kasar RTB ta nunar da cewar tattaunawar da za a yi a birnin Ouagadougou za ta samu halartar 'yan siyasa da shugabannin kungiyoyin farar hula na Burkina Faso domin amincewa da yarjejeniyar mika mulki.

Dama dai shugaban Burkina Faso da aka nada a hukumance a ranar Laraba da ta gabata Kyaftin Ibrahim Traore, ya ba da tabbacin hanzarta mika mulki bayan da ya hambarar da Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda shi ma ya kifar da  zababben shugaban kasar Roch Marc Christian Kaboré biyo bayan tabarbarewar tsaro.

A cikin 'yan watannin baya-bayannan dai, hare-hare sun yawaita a arewaci da gabashin kasar Burkina Faso, inda a yanzu haka garuruwa da dama ke karkashin ikon masu ikirarin jihadi.