1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen bautar da yara kanana

Aliyu Muhammad Waziri RGB
June 12, 2018

Ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara, Majalisar Dinkin Duniya ta ware ta ne domin yakar dabi’ar saka yara aikin karfi a fadin duniya, amman har yanzu ana samun karuwar matsalar a Najeriya.

Tödliche Kinderarbeit in Nigeria Minen
Hoto: DW/A. Kriesch

Duk da kokarin da mahukunta a Najeriyar ke yi, har yanzu ana cigaba da samun dai-daikun jama'a da kungiyoyi da ma kamfanoni da suka yi biris da irin wadannan kiraye-kirayen na cire yara daga kangin bauta. Za'a iya cewa cikin shekaru goma sha shida da kirkiro da wannan rana ta yakar dabi'ar bautar da yara a tsakanin al'umma, ba'a kai ga cimma nasarar da ake hankoro ba a Najeriya sakamakon yadda ake ci gaba da bautar da yara a fannoni daban-daban.

Gwamnati na daukar mataki

Wata yarinya da ke aiki a mahakar ma'adinaiHoto: DW/A. Kriesch

A Najeriya, gwamnatin jihar Bauchi, ta yi kyakyawan tanadi domin ganin ta fidda manyan goben daga cikin harkar bauta, inda tuni ma ta kirkiri wata doka da za ta hukunta dukkan wanda aka samu da laifin bautar da yaran, kamar yadda Muhammad mai Saleh Darakta mai kula da harkokin yara a ma'aikatar kula da lamuran yara da mata a jihar Bauchin ya bayyana. Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da aikin fadakar da al'umma don ganin sun ceci rayuwar yara kanana daga wannan dabi'a da ke matukar haifar da tarnaki ga ci-gaban yaran. Ana sa yara masu kananan shekaru yin aikin karfi kamar hakar ma'adinan karkshin kasa ko noma da leburacin da makamantansu a sassa daban- daban na kasashen Afirka.