1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yaki da cutar maleriya ta duniya

Gazali Abdou Tasawa
April 25, 2019

Bikin ranar ta bana ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara tsakanin likitoci kan sahihancin wasu sabbin magungunan maleriyar kamar Artemisia.

Anopheles stephensi Moskito Mücke
Hoto: picture-alliance/dpa/J.Gathany

Sakamakon karshe na binciken da hukumar lafiya ta duniya ta gudanar a shekarar 2018 ya nunar da cewa babu wani muhimmin cigaba da aka samu a fagyen yaki da cutar maleriya a shekaru hudu na baya bayan nan. An kiyasta cewa daga 2015 zuwa 2017 mutane 435,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a sakamakon kamuwa da cutar ta zazzabin cizon sauro, kuma ko a shekara da ta gabata kusan adadin wadanda cutar ta kashe bai sauya ba.

Sai dai kuma ranar yaki da cutar ta maleriya ta bana ta zo ne a daidai loakcin da ake ci gaba da tafka muhawa tsakanin wasu manyan likitoci da hukumar lafiya ta duniya kan amfani da maganin da ake sarrafawa da itaciyar da aka fi sani da Artemesia da wasu likotoci ke yi wajen yi wa mutanen da suka kamu da zazzabin cizon sauron magani.

Allurar maganin maleriya a KenyaHoto: AP

Likitoci da dama ne ke amfani da ruwan ganyen wannan itaciya ta Artemesia wacce wasu likitocin suka yi ittafakin cewa na kunshe da wani sinadari wanda ke maganin cutar ta maleriya. Sai dai kuma hukumar lafiya ta duniya da wasu likitocin na tababa kan cewa amfani da wannan magani na Artemesia shi kadai na warkar da cutar zazzabin cizon sauron. Dr Hermann Sorgho na cibiyar binciken kimiyya a fannin kiwo lafiya ta Jami'ar birnin Ouagadougou na Burkina Faso na daga cikin masu wannan tababa kan ingancin maganin na Artemesia.

"A kimiyance babu wasu hujjoji da ke nuni da cewa Artemesia na warkar da maleriya. Don haka kwararrun likitoci da dama na ba da shawarar kada mutum ya yi amfani da wannan magani wajen neman waraka daga cutar. Yanzu haka dai akwai bukatar karin bincike da ake yi na ganin ta yaya za a iya hada wannan magani na Artemesia da wasu magungunan ko wasu ganyen itatuwan na daban a wuri daya domin yakar cutar maleriyar. Ta haka ne kadai hankalin jama'a zai iya kwantawa."

Yaduwar cutar maleriya a kasar GambiyaHoto: picture-alliance/dpa

A nasa bangaren kamfanin sarrafa maganin na Artemesia wanda ke da rassa a wasu kasashen Afirka da kuma ya share shekaru biyar yana tallata wannan magani na Artemesia na da yakinin cewa maganin yana warkar da cutar maleriyar. Antoine Djamah shi ne wakilin kamfanin na Artemesia a kasar Togo:

"Akwai nau'in itaciyar ta Artemesia da ake kira Annua wacce ta kunshi sinadarin Artemisinine, akwai kuma wani nau'in itaciyar na Afirka da ake kira Affa wanda yau shekaru sama da 100 kenan da ake amfani da shi a gabashin