Duniya: Ranar yaki da HIV/AIDs ko SIDA
December 1, 2021A cewar Hukumar Yaki da Kwayar Cutar HIV/AIDs din ko kuma SIDA ta Najeriya da Asusun Kula da Ilimin Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ya zuwa yanzu Najeriya ce kasar da ke kan gaba tsakanin kasashen duniya wajen mutuwar yara sandiyyar cutar mai karya garkuwar jiki. A cewar masu yaki da cutar da ma wadanda ke dauke da ita, wannan labari ba mai dadi ba ne kuma ya tayar da hankali. Masana kiwon lafiya kamar Dakta Yarma Ahmad Adamu babban daraktan Asibitin Yarma, na da ra'ayin rashin shan magunguna da kuma jahiltar wannan cuta musamman a yankunan karkara na daga cikin musabbabin samun yawaitar mace-macen yaran.
Babban misali da za a yi shi ne a jihar Borno akwai mutane sama da dubu 60 da ke dauke da kwayar cutar HIV/AIDs ko kuma SIDA, amma wadanda yanzu haka suke karbar magani ba su wuce mutane dubu 12 ba, kamar yadda Alhaji Barkindo Umar Sa'idu shugaban hukumar yaki da cutar ta HIV/AIDs ko SIDA na jihar Bornon ya bayyana. Sai dai a cewar Malam Hassan Mustapha shugaban kungiyar masu dauke da wannan cuta na shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya, matsalolin tsaro na daga abubuwan da suka haddasa yawaitar mace-macen yaran. Bikin ranar yaki da kwayar cutar mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDs ko kuma SIDA na wannan shekarar, na zuwa ne a daidai lokacin da aka cika shekaru 40 da bullar cutar da ake neman mafitaa kanta a duniya. Sai dai har yanzu akwai wadanda suke jahiltar wanzuwar wannan cuta ko kuma tunanin yayin ta ya wuce, abun da ake ganin shi ne musabbabin karuwar mace-macen yara sandiyyar ta.