1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin ranar yaki da jahilci

Ramatu Garba Baba
September 8, 2022

A ranar takwas ga watan Satumba ta kowacce shekara ake gudanar da ranar yaki da jahilci a duniya bisa tsarin hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da kuma al'adu.

Malawi Schulkinder lernen Englisch und Chichewa
Hoto: Andrea Hanks/UPI Photo/Newscom/picture alliance

A  yayin da ake tuni da zagayowar ranar yaki da jahilci a fadin duniya, a Nijar kasar da galibin jama'ar ta ba su je makaranta ba duk da cewa ilimi na sahun gaba wajen ci gaban rayuwar dan adam, sai ga shi an wayi gari gwamnatin kasar ta saka kungiyoyi masu zaman kansu da dai sauran su cikin  tafiyar da tsarin a fannoni dabam-daban don dorewarsa.

An dai kebe ranar domin nuna muhimmancin ilimi a tsakanin al'umma baki daya, kuma an fara gudanar da bikin zagayowar wannan ranar a shekarar 1965. Masana a Najeriya da Nijar na cewa, batun yaki da jahilci na fuskantar kalubale a yankunan kasar da dama a sakamakon aiyukan masu gwagwarmaya da makamai da ake adawa da ilimin boko.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna