1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar zaɓen shugaban ƙasa a Kamaru

August 30, 2011

Shugaba Paul Biya ya tsayar da bakwai ga watan oktoba a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a kamaru. Ya zuwa yanzu shugaban mai shekaru 78 da haihuwa bai bayyana ko zai tsaya takara koko a'a ba.

Paul Biya Präsident Kamerun
Shugaba Paul Biya a zauren mashawartar MDDHoto: AP

Hukumomin kamaru sun tsayar da tara ga watan oktoba a matsayin ranar da za a gudanar da zagaye ɗaya tilo na zaɓen shugaban ƙasa da ke zama na huɗu tun bayan da ƙasar ta rungumin tsarin jam'iyu barkate a farkon shekarun 1990. Shugaba Paul Biya da ya sa hannu kan wannan dokar ya ƙayyade takwas na safe zuwa shida na yamma a matsayin lokacin da waɗanda suke da kati za su iya kaɗa ƙuri'unsu, domin zaɓen wanda zai ja ragamar mulkin kasar na shekaru bakwai masu zuwa.

Wasu ƙananan jam'iyun Kamaru sun riga sun sanar da mutanen da za su tsaya musu takara a zaɓen mai zuwa. Sai dai ita jam'iyar RDPC ko CPDM da ke kan karagar mulki za ta gudanar da babban taronta a ranakun 15 da 16 ga watan satumba domin fit da gwaninta. Shugaba Paul Biya mai shekaru 78 da haihuwa bai bayyana ko zai tsaya takara koko a'a ba. amma kuma minsitan ilimi mai zurfi, kana darekta watsa labarai na jam'iyar da ke kan karagar mulki, Jacques Fame Ndongo ya ce bisa ga dokokin RDPC ko CPDM Paul Biya ne kaɗai ke da hurumin tsayawa takara.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW