1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rangadin ministan harkokin wajen Jamus nahiyar Afirka

February 18, 2015

Frank-Walter Steinmeier zai kai ziyara kasashen Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da Ruwanda da kuma Kenya.

Bundesaußenminister Frank-Walter Steinmeier in Südafrika
Hoto: picture-alliance/dpa

Da yammacin wannan Laraba ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya tashi zuwa ziyarar aiki a wasu kasashen Afirka guda uku da suka hada da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da Ruwanda da kuma Kenya. A cikin wata sanarwa Steinmeier ya ce manufofin ketare ba su tsaya kan neman hanyoyin warware rikici a diplomasiyance ba. Wannan ziyarar ita ce ta hudu da ministan harkokin wajen na Jamus zai kai nahiyar Afirka.Ya ce ko da yake zai ci gaba da sanya ido kan rikicin Ukraine a lokacin rangadin amma bai kamata rikicin Ukraine din ya shagaltar da duniya daga yin hobasa a kan wasu lamurra ba. Ya ce huldar dangantanku tsakanin Jamus da Afirka ta wuce maganar kandagarkin rikice-rikice da hadin kai da kuma taimakon tattalin arziki. Ya ce Afirka na da kyawawan damarmaki ga kamfanonin Jamus wanda zai mayar da hankali kansu a rangadinn zuwa kasashen na Demokradiyyar Kwango da Ruwanda da kuma Kenya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar