Rangadin Westerwelle da Niebel a Gabas ta Tsakiya
June 14, 2011Ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle tare da takwaransa mai kula da taimakon raya ƙasa Dirk Niebel, sun fara wani rangadi a yankin Gabas Ta Tsakiya, da zumar bada shawarwari a rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Isra'ila da Falesɗinu.
Nan gaba a yau za su gana da shugaban Hukumar Falesɗinawa Mahamud Abbas kamin daga bisani su tattauna da hukumomin bani yahudu. Sannan zasu ziyarci Gaza domin tantance irin taimakon da Jamus za ta iya kai ma wannan yankin da ke fama fa matsaloli.
A yayin da yake hira da 'yan jarida jim kaɗan kamin ziyarar Weterwelle ya hurta cewa: " Za mu yi kira ga ɓangarorin biyu su bada haɗin kai a cimma zaman lafiya, idan kowa yayi tsayuwar gwamen jaki, abin ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Ya zama wajibi a samu ƙasashe biyu masu cikkaken 'yancin, waɗanda za su yi makwabtaka da juna cikin girma da arziki."
A ɗaya wajen, ministocin zasu kira ga Isra'ila ta cire takunkumin da ta sakawa zirin Gaza sannan su kuma 'yan sari ka noƙen Hamas su daina kai hare-hare ga Isra'ila.
Mawallafi: Yahouza Sadissou MadobiEdita: Abdullahi Tanko Bala