China da Rasha na kawo cikas ga G20
March 2, 2023![Indien G20-Treffen in Delhi](https://static.dw.com/image/64859122_800.webp)
Talla
Tuni da jagoran diflomasiyyar Amirka Antony Blinken da ake sa ran zai halarci taron,ya yi gargadin cewar ba zai gana ba da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a wannan ganawar ta kwanaki biyu tsakanin ministocin harkokin wajen na G20. A ranar Asabar, taron ministocin kudi na G20 an waste hannun riga saboda China da Rasha sun ki amincewa su saka hannu a kan sanarwar bai daya ta karshen taron.