1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan tawayen Libiya

July 29, 2011

Mutuwar kwamandan 'yan tawayen Libiya janar Abdel Fatah Younes, na ci gaba da haddasa kace-nace a tsakanin 'yan tawayen

Marigayi Abdel-Fattah YounisHoto: dapd

Marigayi Janar Abdel Fatah Younes dai wanda shine tsohon ministan harkokin cikin gidan Libiya gabannin ɓallewar sa zuwa ɓangaren 'yan tawayen ƙasar dake hamɓarar da shugaba Mouammar Gaddafi dai, ya kasance mutum na biyu mafi girman muƙami kafin ya sauya sheƙa zuwa ɓangaren 'yan tawaye, ya mutu ne a wani yanayi mai cike da sarƙaƙiya.

Wasu 'yan bindiga ne dai suka harbe janar Abdel Fatah Younes, bayan da majalisar masu adawa da mulkin shugaba Gaddafi sukayi sammacin sa daga fagen fama domin tattauna wasu batutuwan da suka shafi dakarun, kamar yadda shugaban majalisar mustapha Abdeljalil ya bayyana:

Kisan da aka yiwa janar ɗin dai tare da wasu hafsoshin sojin 'yan tawayen su biyu ,yana zaman wata alamar rarrabuwar kai atsakanin yan tawayen dake faftukar hambarar da shugaba muammar Gaddafi daga karagar mulki.

Hoto: dapd

A lokacin da yake bayyana mutuwar, kwamadan shugaban majalisar 'yan tawayen mustapha Abdel Jalil ya bayyan cewa tuni aka cafke wanda ya ƙaddamar da wannan kisan gilla. Ya kuma ce zasu ware kwanaki uku domin yin zaman makoki duk da cewar har zuwa lokacin da yake wannan bayani ga manema labarai ba'a gano gawar marigayin ba.

"Yace, da farko zamu ƙaddamar da kwanaki uku na zaman makoki, abu na biyu kuma, zamu haɗa karfin mu wuri guda domin kamo masu hannu cikin wannan aika aika ,abu na uku kuma, wannan wani gargaɗi ne ga dukkan sojojin dake cikin birnin."

Wasu rahotannin da har yanzu ba'a tabbatar da sahihancinsu ba sun bayyana cewa, su 'yan tawayen da kansu ne suka cafke shi wannan kwamnadan suka kuma bindige shi, bayan da aka sami rahotannin cewa har yanzu Iyalansa suna da alaƙa da muammar Gaddafi lamarin da ake masa kallon jemage wanda bashi da tsayayyar alƙibla tsakanin 'yan tawayen da kuma ɓangaren shugaba Ghaddafi.

Sai dai kuma matuƙar ta tabbata cewa yan tawayen sun fara faɗa a tsakanin su,to babu makawa hakan zai zama wata babbar koma baya a tsakanin su wanda kuma ka iya zama wata barazana ga ƙasashen yammacin duniya su amince da majalisar a matsayin wadda ke zama ɗaya tilo mai faɗa-aji a ƙasar.

A waje guda kuma shugaban majalisar mustapha Abdel Jalil yana ta ƙoƙarin toshe wannan ɓaraka, yana mai cewa wannan wata jita-jita ce da dakarun Gaddafi,ke yaɗawa domin raba kan 'yan tawayen. Jim kaɗan bayan wannan ganawa da shugaban 'yan tawayen yayi da manema labarai, sai wasu motoci biyu ɗauke da manyan bindigogi suka yiwa hotel ɗin da akayi ganawar tsinke suna harbi cikin iska.

Wasu daga cikin 'yan tawayen Libiya suna zanga-zangaHoto: picture-alliance/dpa

Wani da akayi abin akan idanun sa ya bayyana cewa, daga bisani waɗannan mutane sun kutsa da makamansu har cikin otal din ,sai dai kafin suyi ɓarna an rarrashe su tare da kwantar musu da hankali, dai-dai lokacin da suke kuwwa tare da kalaman cewa majalisar 'yan tawayen itace ta hallaka janar Younes.

Marigayi janar Abdel Fatah Younes dai, shine ministan harkokin cikin gida na gwamnatin Gaddafi kuma mutum na biyu mafi girman muƙami a gwamnatin, kafin ɓallewarsa cikin watan Fabrairun daya gabata. Ya kuma koma ɓangaern 'yan tawayen har takai shine kwamandan su.

Har zuwa yanzu ƙasashen Amirka da Turai ke mara musu baya domin hamɓarar da Muammar Gaddafi daga mulkinsa, lamarin da har zuwa yanzu haƙarsu bata cimma ruwa ba.

A ranar Alhamis (28.07.11) ma dai an jiyo ƙarar fashewar wasu nakiyoyi ukku a birnin Tripoli na ƙasar, a yayin da gidan telebijin ɗin ƙasar ya ruwaito cewa jiragen saman yaƙi na shawagi a saman birnin inda nan ne dakarun ƙungiyar ƙawancen tsaro na NATO ke kai hari.

Mawallafi : Nasiru Salisu Zango

Edita : Saleh Umar Saleh