1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rarrabuwar kawuna kan takarar Jonathan a 2015

June 19, 2013

'Ya'yan jam’iyar PDP na arewa maso yankin tsakiyar Najeriya sun nisanta kansu da sanarwar ba wa Jonathan 'yancin takarar shugaban kasa a zaben 2015.

Hoto: DW/U.Haussa

Jihar Naija na daya daga cikin jihohin da ke tinkaho da shugabanni ko jiga-jigan jam'iyar PDP mai mulki, da ta hada da mutane irin su tsoffin shugabannin kasa Ibrahim Babangida da Abdulsalam Abubakar da kuma shugaban gwamnonin Arewacin kasar Muazu Babangida Aliyu, wanda tun lokacin da ya ce akwai yarjejeniyar wa'adi da ya ba shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya amince da shi da kuma goyon baya ga gwaman jihar Rivers a matsayin shugaban gwamnonin kasar ne, ya shiga jerin 'ya'yan jam'iyar da ake takun saka da su a tsakaninsu da mahukunta a Abuja.

Kwanan daya bayan da wasu shugabanin jam'iyar ta PDP suka ce, al'umomin yankin arewa maso tsakiyar Najeriya sun amince da takarar shugaba Jonathan ne dai, wasu magoya bayan jam'iyar ta PDP da kuma dattawan jihar Naija suka nisanta kansu da sanarwar kungiyar da ta kunshi 'yan yankin south-south da North central da middle belt, na goyon bayan takarar Jonathan a zaben 2015.

A karshen wata ganawa da shugaban kasa ne dai kungiyar da ta kunshi Chief Edwin Clerk mai goyon bayan Jonathan da kuma Emeh Ebote, tsohon shugaban majalisar dattijai, suka ce al'umar wannan yanki na goyon bayan Jonathan a zabe mai zuwa.

To sai dai al'umomin wannan yanki sun ce an ari bakinsu ne an ci masu albasa, domin su har yanzu su na tare da shugaban gwamnonin arewacin kasar dari bisa dari, kamar yadda mai bai wa gwamnan shawara akan harkokin majalisa  Abdulhameed Elwazir ya ke cewa.

Hoto: DW/U.Haussa

 "Shi dai Edwin Clerk dottijo ne da ada ake bashi girma, amma wannan magana da bai yi shi da yawun mu ba, domin bisa ga dukkan alamu, akwai wata manufa wanda shi ne kadai ya sani".

Mai da martani tsakanin bangaren 'yan tazarce na shugaban kasa da kuma bangaren 'yan canji dai abu ne da yanzu ya dauke hankalin 'yan Najeriya, abun da kuma ya sa wasu 'ya'yan jami'iyar ta PDP irin su gwamna Babangida da ke zama shugaban gwamnonin arewa yin bakin jinni, sai dai wannan bai hana 'ya'yan jam'iyar daga arewa cigaba da goyon bayansu ba ga gwamnan kamar dai yadda ma'ajin jam'iyar a jihar Naija Yusuf Tanko Pandogari ke cewa

 "Idan akwai dubu bisa dubu muna goyon bayan shugaban gwamnonin arewa, domin maganar da ya fadi ita ce gaskiya, kuma wa'yancan basu da wakilcin kowa".

Sai dai kuma duk da matakan da jam'iyar ta PDP ke dauka na ganin an kawo karshen rikicin jam'iyar, bisa ga dukkan alamu akwai sauran rina a kama, musanman idan aka yi la'akari da rarrabuwar kawunan da ke tsakanin gwamnonin kasar da bangaren shugaban kasa, kamar yadda taron gwamnonin na baya-bayan nan da kuma kalaman wasu gwamnonin da magoya bayansu ke zama 'yar manuniya.

To ko ina talakawa suka karkata game da wannan danbarwa? i Hassan Muhammadu Saba na cewa "idan zaka iya tunawa lokacin zabe bai yi ba, kuma shugaban zabe ya ce kada kowa ya fara yakin neman zabe, saboda haka bamu san inda suka samu amincewar tsaida Jonathan a matsayin dan takara ba".

Neman Tazarce: Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: AP

Yanzu dai abin jira a gani shine ko matakin da jam'iyar ta PDP ke dauka zai taimaka wajen magance rikicin cikin gidan da ya mamaye ta ko kuma a'a.

Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Zainab Mohammed Abubakar