1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Babu batun janye soji daga Zaporizhzhia

Binta Aliyu Zurmi
November 28, 2022

Rasha ta ce babu batun ficewar dakatunta daga yankin gabashin Ukraine inda tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia da ke zama mafi girma a nahiyar Turai ta ke.

Ukraine | Atomkraftwerk Saporischschja
Hoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Kremlin ta jaddada cewar har yanzu tashar makamashin na karkashin ikon Rasha kuma za ta ci gaba da zama karkashin ta don gujewa barazanar kai hari.

Sanarwa na zuwa ne a dai-dai lokacin da mahukuntan Ukraine suka ce sojojin Rasha na shirin ficewa daga yankin.

Dukkanin bangarorin biyu na masu ikirarin samar da cikaken tsaro a yankin da suke zargin juna da yunkurin kai hari a kan tashar makamashin. Rasha da Ukraine sun yi gargadi kan girman hadarin da ke tatare da makamshin nukiliya. 

A watan Satumba nan ne Rasha ta sanar da shigar da yankin na Zaporizhzhia da wasu yankunan Ukraine a cikin kasarta a hukuman ce.