1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Mali sun gamsu da sulhu kan Nijar

September 11, 2023

Shugaba Vladimir Putin na Rasha da takwaransa na Mali Assimi Goita sun jaddada goyon bayansu na a warware dambarwar juyin mulkin Nijar cikin ruwan sanyi.

Rasha da Mali sun yi watsi da matakin sojaHoto: Francis Kokoroko/REUTERS

Shugabannin biyu sun jaddada wannan matsaya ne a yayin tattaunawa ta wayar tarho da suka yi a ranar Lahadi (10.09.2023) kamar yadda fadar Kremlin ta Rasha ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin da suka kifar da gwamanati Mohamed Bazoum suka zargi Faransa da shirya kai wa Nijar hari ta yi amfani da wasu kasashen ECOWAS.

Karin bayani: Sojin Nijar: Faransa ta fara jibge makaman kai mana hari

A gefe guda kuma Shugaba Putin da Assimi Goita sun tattauna kan huldar Rasha da Mali a fannin tattalin arziki da kuma yaki da ta'addanci a daidain lokacin da kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma 'yan tawayen Azawad suka fara tayar da kayar baya a Arewacin kasar biyo bayan fatali da yerjejeniyar Algiers.

Karin bayani: Mali za ta mutunta yarjejeniyar Algiers

Shugaban mulkin sojan na Mali ya kuma yi godiya ta musanman ga Rasha bisa goyoyn bayan ta ba wa Bamako a lokacin kuri'ar da aka kada a zaman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan bukatar ficewar dakarun MINUSMA daga kasar.