Siriya: Rasha da Turkiyya za su gana
December 29, 2018![Litauen Exercise Baltic Operations | US-Soldaten bei Landung](https://static.dw.com/image/46623708_800.webp)
Talla
Shugaban kasar Amirka Donald Trump dai ya bayyana shirin kasarsa na janye sojojinta da ke kasar Siriya da yawansu ya kai 2000, da nufin kawo karshen tsare-tsaren Amirka a yankin Gabas ta Tsakiya. A wani sabon labarin kuma, Amirkan na sake duba batun janye sojojinta da ke aikin yaki da ta'addanci a kasar Afghanistan wadanda yawansu ya kai 7000, duk kuwa da cewar 'yan ta'adda na ci gaba da kai farmaki a wasu yankuna na kasar ta Afghanistan.