1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Tashin hankali na ruruwa a tsakanin Rasha da Ukraine

April 1, 2021

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya sanar cewa ci gaba da samun zaman dar-dar a yankin gabashin kasar na nuna cewa kasar Rasha na yunkurin saba yarjejeniyar zaman lafiyar da suka kulla.

Ukraine | Präsident Wolodymyr Selenskyj in Donezk
Hoto: Ukrainian Presidential Press Office/AP Photo/picture alliance

Zelenskiy ya zargi Rasha da jibge dakarun soji a kan iyakar Ukraine. Sai dai mai magana da yawun gwamnatin Rasha Damitry Peskov ya musanta wannan zargin.

''Rasha tana tura dakaru ne a cikin kasarta. Bai kamata wani ya nuna damuwa  a kan hakan ba. Kasarmu ta Rasha na daukar matakan kare iyakokinmu ne.'' inji Mr. Peskov


Ukraine da Rasha sun fara samun takun-saka a shekara ta 2014 lokacin da Rasha ta mamaye yankin Crimea, kuma ana zargin hukumomin Rasha sun bayar da gudunmawa ga 'yan tawaye a yankin Donbass na Ukraine don tayar da zaune tsaye. Daga baya an kulla yarjejenyiar zaman lafiya amma kuma a baya-bayan nan Ukraine ta yi zargin an kashe mata sojoji guda hudu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW