SiyasaTurai
Rasha da Ukraine na tattaunawar dakatar da yakin da suke yi
June 2, 2025Talla
Turkiyya ta ce wakilan Rasha da na Ukraine za su gabatar da dukkan bukatunsu na ganin an dakatar da yakin da suke gwabzawa sama da shekaru uku, a yayin taron tattaunawar cimma yarjejeniyar zaman lafiya a wannan Litinin a birnin Santambul.
Ministan harkokin wajen Trukiyya Hakan Fidan, wanda zai sa ido kan ganawar da wakilan ke shirin yi a karo na biyu tun bayan barkewar yakin a cikin shekarar 2022, ya ce ganawar keke-da-keken za ta taimaka matuka wajen samun masalahar dakatar da yakin.
Karin bayani:Jamus za ta taimaka wa Ukraine da makaman yaki
Gabanin fara taron, sai da wakilin Ukraine suka gana da na kasashen Jamus da Italiya da kuma na Burtaniya, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Ukraine ta tabbatar.