1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Ukraine na zargin Juna kan Kherson

Ahmed Salisu
September 18, 2022

Kasashen Rasha da Ukraine na ci gaba da zargin juna kan jawo barin wutar da aka yi a birnin Kherson da ke kudancin Ukraine, bayan da wani faifen bidiyo ya nuna yadda aka yi taho mu gama tsakanin bangarorin biyu.

DW Still | Krieg in der Ukraine - Soldat im Schützengraben
Hoto: DW

Wata kafar yada labarai ta Rasha ta ce an yi arangama tsakanin dakarun Rasha da na Ukraine a wata tashar jirgin kasa, inda rahoton ya ce sojin Rasha sun fatattaki na Ukraine, sai dai ya zuwa yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labarin.

Da safiyar wannan Lahadi, mai magana da yawun rundunar sojin Ukraine a kudancin kasar Natalie Gumeniuk ta ce Rasha ce ta haifar da harbe-harben da aka yi kuma dama ta ce ta sanar da yiwuwar faruwar hakan a kwanakin baya, inda ta kara da cewar an kitsa hakan ne don a zubar da mutuncin sojin Ukraine.