Ci gaban rikicin Rasha da Ukraine
March 10, 2022Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce kasarsa za ta koma kan kafafunta da kuma zama mai cikakken iko, idan al'amura suka saisaita. A cewarsa kasashen yamma sun hada karfi waje guda, suna kakabawa Rashan Takunkumi, kuma koda ta kai hari Ukraine ko ba ta kai ba da ma suna da niyyar sa mata Takunkumai kuma babu makawa sai sun saka mata.
Takunkumin kasashen wajen a kan Rasha dai yana matukar shafar tattalin arzikin Moscow, inda tuni darajar kudin kasar ta yi mummunar faduwa yayin da ake fargabar karewar wasau abubuwa a shagunan kasar. Tuni dai dubban 'yan gudun hijira ke kauracewa kasar Ukraine din domin tsira da rayukansu, sakamakon hare-haren da dakarun Rasha ke kaiwa babu kakkautawa.
An dai gaza cimma matsaya a karo na uku, yayin taron tattaunawa domin shawo kan rikicin tsakanin Rashan da makwabciyarta Ukraine. Taron karo na uku dai, ya gudana a kasar Turkiyya tsakanin mininstan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya ciki har da Majalisar Dinkin Duniya, ke nuna bacin ransu kan harin bam da ya yi sanadiyar mutuwar yara uku a asibitin yara da ke birnin Kyiv.