Hari a sansanin soji ya hallaka jami'an tsaro
December 26, 2022Talla
A cewar ma'aikatar tsaron wannan shi ne karo na biyu da sojojin Ukraine ke amfani da jirgi mara matuki a yunkurin kai hari a sansanin sojoji da ke kudu maso gabashin birnin Moscow a wannan wata.
Wannan yunkurin hari har sau biyu na nuna alamar yadda Rasha ke fuskantar kalubale, duk da cewa Ukraine ba ta fito ta dauki alhakin harin ba, amma sun bayyana cewar ramuwar gayyace a kan mamayar da Rasha ke ci gaba da yi a ka
sarsu.
Rasha na ci gaba da kaddamar da hare-hare a manya da kananan birane a cikin Ukraine, ko a karshen makon da ya gabata an kai wani mumunan hari a Kherson inda mutum 10 suka rasa rayukansu yayin da wasu 58 suka jikkata sakamakon hari ta sama.