1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Ukraine hare-hare na kara tsananta a Kherson

Abdoulaye Mamane Amadou Zainab Moh' Abubakar
October 19, 2022

Rasha na shirin kwashe fararen hula da ke birnin Kherson da zummar kubutar da su daga fafatawar da ke yin tsanani tsakani dakarunta da na Ukraine.

Jagoran Cherson, Vladimir Saldo
Jagoran Cherson, Vladimir SaldoHoto: Maksim Blinov/Sputnik/AP/picture alliance

Babban hafsan sojin Rasha da ke jagorantar yaki a Ukraine, ya ce yunkurin Moscow shi ne na ganin mutanen sun tsira daga yaki ta hanyar ba su cikakkiyar kariyar da ta dace duba da yadda dakarun Ukraine ke mar da martani mai tsanani da muggan makamai a Kherson ba kakkautawa. Kana madugun yakin ya zargi Ukraine da yin luguden wuta kan gidajen jama'a har ma da wasu fannoni na samar da wutar lantarki.

A wani jawabinsa na rana tana shugaba Volodymyr Selensky caccaki abinda ya kira kasawar da Moscow ta fara nunawa a fagen daga, inda ya zargeta da neman dauki daga Iran ta hanyar jirage maras matuka don kaddamar da hare-harenta na baya-bayan nan, lamarin da Shugaba Selensky ya kira abin kunya. Rashar dai ta kara tsananta barin wutar da ta ke yi a baya-bayan nan kan wasu muhimman biranen Ukraine ciki har da birnin Kiev.