Rasha na ci gaba da kai hare-hare a Ukraine
March 1, 2022Talla
A wannan rana ta shida ta mamaya, Rasha ta yi ruwan bama-bamai a tsakiyar Kharkiv, birni na biyu mafi girma a kasar Ukraine, a daidai lokacin da kasashen yammacin duniya ke kara kakaba mata takunkumi.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Ukraine ta fitar, ta bayyana cewa Rasha ta tura motocin sulke, da makamai atilari domin yin mata kawanya da nufin mayar da biranen Kiev da Kharkiv da Odessa da Kherson da Mariupol karkashin ikonsu.
Gwamnan yankin Donetsk ya nunar da cewa an katse wutar lantarki a babban tashar jiragen ruwa na Mariupol da ke Kudu maso gabashin Ukraine. kasar dai ta bayar da rahoton mutuwar fararen hula 352 yayin da wasu 2,040 suka jikkata tun bayan mamayar, sannan ta ce dubban sojojin Rasha sun halaka.