1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na duba yiwuwar kai wa Siriya gudummawa

Zulaiha Abubakar
April 23, 2018

Ministan harkokin kasashen wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewar kasar na duba yiwuwar kai wa kasar Siriya gudummawar makamai masu linzami.

Ministan harkokin kasashen wajen kasar Rasha
Sergei LavrovHoto: Reuters

Ya kuma kara da cewar Rasha za ta bayyana wa duniya irin makaman da zarar ta cimma matsaya kan batun a yayin da yake ganawa da manema labarai, a cikin makon da ya gabata ne ministan ya bayyana cewar tun da kasashen yammacin Turai suka yi watsi da gargadin da Rasha ta yi musu a kan kai hari kasar Siriya. To ya zamar wa Rasha wajibi a matsayin ta na babbar mai goyon bayan shugaba Bashar al-Assad na Siriya ta bashi taimakon jiragen yaki nan ba da dadewa ba.