Gazprom na shigar da gas Turai
March 14, 2022Talla
Duk da rikicin da ake na Ukraine da kuma takunkumin karya tattalin arziki da kasashen yammacin duniya suka kakaba wa Rashar. kamfanin Gazprom ya ce sun ci gaba da aikin isar da gas din a nahiyar Turai. Kamfanin ya ce farko lokacin da dakarun Rasha suka kai hari a Ukraine, an dan samu damuwa na 'yan kwanaki na katsewar isar da iskan gaz din, amma daga baya kamfanin ya koma aikinsa. Kamfanin na Gazprom ya ce a kowacce rana sama da murabba'in cubic miliyan 109 na iskan gaz din suke shigar da shi a nahiyar turai Turai ta hanyar Ukraine.