1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Rasha na matsa kaimi a Ukraine

Abdourahamane Hassane
February 24, 2022

Mace-macen fararen hula na karuwa a Ukraine a daidai lokacin da sojojin Rasha ke ci gaba da kai farmaki a wasu manyan birane na kasar.

Ukraine Russland Krieg Angriff in Charkiw
Hoto: Sergey Bobok/AFP

Rahotannin sun nunar da cewa kawo yanzu mutane kusan ubu biyu suka mutu a Ukraine, sakamakon hare-haren da sojojin Rasha ke ci gaba da kai wa. Mahukuntan Ukraine sun tabbatar da cewa, dakarun Rasha sun karbe iko da garin Kherson da ke yankin kudancin kasar. Shugaban yankin Gennady Lakhuta ne ya tabbatar da hakan, inda ya nunar da cewa sojojin sun mamaye baki dayan birnin da ke da yawan mutane dubu 290 kana ba shi da nisa da yankin Crimea da yanzu haka yake karkshin ikon Rasha. Birnin na Kherson dai na zaman birnin na farko da Rashan ta kwace iko da shi.Mun tanadar muku da jerin rahotani daga kasa

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna