1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Rasha na nazari kan gwamnatin Taliban

August 26, 2021

Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta sanar da cewa za ta ci gaba da bibiyar abubuwan da ke faruwa a Afghanistan kafin ta amince da mulkin Taliban a hukumance.

Russland | Moskau | PK Angela Merkel und Wladimir Putin
Hoto: Mikhail Metzel/ITAR-TASS/imago images

Mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya sanar da cewa za su sanya ido su ga yadda Taliban za su kare rayukan mutanen Afghanistan da jami'an jakadancin Rasha a kasar kafin ta sanar da amincewa da gwamnatin ta Taliban. 

Hukumomin na Rasha sun ce suna son ganin zaman lumana ya dawo wa Afghanistan kuma suna fatar za a dakatar da kwararar muggan kwayoyi daga kasar.