1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta fusata da karbe wa Ukraine yankunanta

Zainab Mohammed Abubakar ZUD/USU
September 30, 2022

Yankuna hudu da gwamnatin Rasha ta sanar da karbewa sun hada da Luhansk da Donetsk da Kherson da kuma Zaporizhzhia wadanda a yanzu aka shigar da su cikin Rasha.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir PutinHoto: Dmitry Astakhov/Sputnik/REUTERS

Shugaban Rasha Vladimir Putin a yayin bikin ayyana shigar da yankunan Ukraine hudu da aka gudanar da zaben raba gardama a cikinsu, a cikin kasarsa, ya ce mataki ne na tabbatar da tsaron al'ummarsa da mutanen da ke yankunan da ya ce suka 'yantar.

Sai dai nan take Amirka ta yi martani kan wannan mataki na Rasha da ta bayyana da "zama karbe yankuna mafi girma a Turai tun bayan yakin duniya na biyu", wanda kuma ke bai wa Moscow iko da akalla kaso 15 daga cikin 100 na Ukraine.

Shugaba Putin na Rasha da mukarrabansaHoto: Mikhail Metzel/AP Photo/picture alliance

Linda Thomas-Greenfield  ita ce jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya ta kuma nuna fushin kasarta a kan matakin na Rasha.

''Muna Allah wadai da wannan aika-aika ta Rasha. Kuma za mu ci gaba da yin aiki tare da abokanmu da takwarorinmu da masu ra'ayinmu don gasa wa Rasha aya a hannu." in ji jakadiyar ta Amirka

Jakadiyar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield Hoto: DAVID DEE DELGADO/REUTERS

Tun da safiyar wannan Juma'ar ce dai Shugaba Putin ya gabatar da doka da ke ayyana 'yancin cin gashin kan yankunan Kherson da Zaporizhzhia, matakin da ya dauka tun a watan Febrairu a kan Luhansk da Donetsk, bayan yankin Cremea da ke zama mafarin girki.

Ra'ayoyi dai sun banbanta game da matakin Rashar a yayin da mafi yawa ke goyon bayan gwamnati, wasu sun nuna adawa, daura da 'yan ba ruwanmu game da wannan rikici.

Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya soki matakin Moscow. Bugu da kari Steltenberg ya yi kira ga Shugaba Vladimir Putin da ya kawo karshen yakin da ya kaddamar a kan Ukraine.