SiyasaTurai
EU: Dabarun rage tasirin Rasha a Afirka
September 13, 2023![EU | Hukumar Tarayyar Turai | Ursula von der Leyen | Afirka | Tasiri | Rasha](https://static.dw.com/image/66796882_800.webp)
Talla
Shugabar Hukumar Tarayyar Turan Ursula von der Leyen ta bayyana hakan ne yayin jawabin da ta gabatar a gban majalisar Tarayyar Turan, inda ta bayar da misali da yankin Sahel da ta ce shi ne mafi talauci kana wanda ke bunkasa a bangaren yawan al'umma. A cewarta yawaitar juyin mulki a yankin, zai sake damalmala al'amura na tsawon lokaci. von der Leyen ta nunar da cewa Rasha na yin tasiri da kuma cin moriyar rudun da ake fama da shi a yankin, tana mai cewa ya kamata kungiyar EU ta nuna hadin kai wajen ceton Afirka kamar yadda ta nuna a kan Ukraine.