1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na yunkurin kare kudurin Majalisar Dinkin Duniya kan Siriya

February 1, 2012

Rasha na neman yin kafar ungulu ga yunkurin Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya a Siriya, maimaimakon sassanta rikicin da ke tsakanin gwamnatin Assad da masu adawa

Demonstrators protest against Syria's President Bashar al-Assad in Jerjenaz, near Idlib January 27, 2012. Picture taken January 27, 2012. REUTERS/Handout (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Masu zanga-zanga a SiriyaHoto: Reuters

Rasha tana ci gaba da hana ruwa gudu a kokarin gabatar da wani kudiri da zai yi barazanar dora takunkumi kan gwamnatin Syria a Damascus, idan har  bata gaggauta kawo karshen  rashin imani da keta hakin yan Adam a kasar, tare da baiwa jama'a karin democradiya ba. Wannan mataki na Rasha ya sanya duk da zaman muhawara da  kwamitin sulhu yayi, babu wani abu sabo da  aka cimma a zauren. Gwamnati a Moscow  tana  tsoron cewar gabatar da irin wnanan kudiri yana iya baiwa kasashen yamma damar katsalandan da karfin soja a Syria, kamar dai irin yadda ya faru a kasar Libya. Bugu da kari kuma, Rashan tana tsoron cewar bayan kawar da Mubarak a Masar da Gaddafi a Libya,  Bashar al-ASsad shi kadai ya rage  mai abokantaka da ita a yankin gabas ta tsakiya Rasha din tana kuma da dangantakar ciniki mai karfi da Damascus sansanin ta na soja a garin Tartus na Syria.  

Wannan matsayi na Rasha ya zama babban kuskure, saboda a yunkurin amfani da ikon  ta na hawa kujerar naki a kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya, a matsayin wata hanya ta ci gaba da  dan abin da ya rage mata na angizo a al'amuran duniya,  tana keta sharudda da dokokin da suka shafi kare mutunci da hakkin yan Adam. Rashan, a wani salo irin na zamanin daular Soviet, tana ci gaba da  goyon bayan dan mulkin kama karya  dake da jinin jama'a a hannuwansa. Goyon bayan da  Moscow ta taba baiwa  Saddam Hussein a Irak, shine yanzu  take baiwa Bashar al-Assad a Syria. Duk da haka, Rashan tana sane da cewar ba zata kasance mai shiga tsakani da neman sulhu na hakika  a Syria ba, sai ta  yi nesa da  shugaba Bashar al-Assad a kwamitin sulhu. Idan har Rashan bata yi haka ba, duk wani mataki da zata dauka, zai zama kamar dai neman  ci gaba da goyon baya ne ga  dan amshin shatan ta a Damascus, wanda yake kara shiga halin matsin lamba ta fuskar soja a kasar sa. Tun a yanzu ma, rahotanni suka ce  mayakan  yan adawa sun isa kusa da   birnin Damascus. Wasu rade-radin sun nuna cewar yanzu haka  kashi arba'in ne cikin dari na  al'ummar Syria suke  goyon bayan shugaban nasu.

To sai dai  Rasha ta maida kanta saniyar ware a kwamitin sulhu, sakamakon matakinta na hana  gabatar da  kudiri kan Syria. Ko da shike China har yanzu tana goyon bayan matsayin na Rasha, amma  mahukunta a Peking sun nuna shirin su na   daidaaitawa da   sabbin masu mulki a duniyar Larabawa, musamman saboda bukatun su na makamashi daga yankin.

Gwamnatin  Putin ya kamata ta gane  wadanda suka nuna goyon bayan su ga kudirin kan Syria, wanda ba kasashen yamma kadai suke goyon bayan sa ba. Kasar Morocco ce ta gabatarwa kwamitin sulhu shi, kuma yana samun goyon baya daga dukkanin kasashen kungiyar  hadin kan Larabawa, wadanda ma suka nemi  Assad ya sauka daga shugabancin Syria, ya mika madafun iko tsakanin kwanaki 15 ga mataimakin sa. Wannan kungiya ta goyi bayan kudirin ne bayan kasa samun nasarar aikin tawagar  yan kallo da ta tura zuwa kasar ta Syria.

Kudirin  na kasashen Larabawa watakila shine dama ta karshe ta hana Syria tsunduma gaba daya  cikikn yakin basasa. Idan har ya mika mulki, Assad yana iya fita daga kasar zuwa gudun hijira a ketare, kamar dai yadda shugaban Yemen yayi, ba tare da an yi amfani da karfi domin aiwatar da canji a tsarin shugabancin kasar ta Syria ba. Yan adawa ana iya  shigar dasu a aiykan mulki,  tare da  kare yancin tsiraru a wannan kasa, yayin da  kasashen Larabawa  zasu  dauki  matsayi na masu  neman  sulhu tsakanin  dukkanin al'ummar kasar ta Syria. To sai dai ga duka wadannan abubuwa Rasha tace Njet, taki: kamar dai  kasar ta Syria zata zama  zakaran gwajin dafi ne na karfi da angizon Rasha, bayan  kawo karshen  zamanin yakin cacar-baka.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal