1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nord Stream: Rasha na zargin Amirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 28, 2022

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce tilas ne shugaban Amirka Joe Biden ya bayar da amsa, in har Washington na da alaka da fashewar bututun Nord Stream da ke safarar makamashin iskar gas daga Moscow zuwa Jamus.

Rasha | Jamus | Iskar Gas | Stream 2 | Nord Stream 1
Butun Nord Stream na tsiyayaHoto: Stefan Sauer/dpa/picture alliance

Cikin wani jawabi da ya yi a watan Fabarairun wannan shekara gabanin mamayar Rasha a Ukraine din dai, Biden ya bayyana cewa bututun Nord Stream zai zama tarihi in har Moscow ta mamaye Ukraine. Mai magana da yawun ma'aikataar horkokin kasashen ketaren ta Rasha Maria Zakharova ce ta bayyana haka a kafafen sada zumunta na zamani, tare da wallafa faifen bidiyo na Shugaba Biden yana mai cewa za su kawo karshen bututun Nord Stream 2 in har tankokin yakin Rasha suka ketara kan iyakokin Ukraine.