NATO ta shiga yakin Ukraine da Rasha
December 1, 2022![Rasha | Sergey Lavrov | Zargi | NATO | Yaki | Ukraine](https://static.dw.com/image/63958108_800.webp)
Talla
Ministan harkokin kasashen wajen na Rasha Sergey Lavrov ya ayyana bai wa Ukraine makamai dankuma bai wa sojojinta horo a matsayin dalilansa na yin wannan zargi. Lavrov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai ta hanyar kiran waya ta bidiyo, inda ya ce ba za a taba cewa Amirka da NATO ba su shiga cikin yakin dumu-dumu ba. Ya nunar da cewa kasashen Jamus da Birtaniya da Italiya, ba wai makamai kawai suke bai wa ssojojin Ukraine din ba har ma da ba su horo a cikin kasashensu.