1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso ta karbi alkama kyauta daga Rasha

Suleiman Babayo ATB
January 27, 2024

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta tabbatar da samun kyautar alkama daga kasar Rasha a matsayin rage radadin tsadar rayuwa da kasashen duniya suke fuskanta sakamakon yaki tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.

Rasha | Hatsi
Hatsin RashaHoto: Sergey Pivovarov/SNA/IMAGO

A wannan Jumma'a da ta gabata kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka ta karbi ton dubu-25 na alkama kyauta a wani bangaren game da alkawarin Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi wa kasashe shida na Afirka. Wani jami'an kasar ta Burkina Faso ya tabbatar da haka.

Shugaba Putin ya yi alkawarin lokacin taron Afirka da Rasha, a birnin Saint Petersburg na kasar ta Rasha, kuma sauran kasashen da aka yi musu alkawarin su ne Mali, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Eritrea, Somaliya and Zambiya.

Haka na cikin matakin da Rasha ta dauka na rage radadin halin da kasashe suka shiga na tsadar hatsi sakamakon yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine.