Rasha ta ce sojojinta sun mutu a Ukraine
January 2, 2023Ukraine ta ce ta hallaka daruruwan dakarun Rasha a daren sabuwar shekara, bayan samun taimakon makaman yaki daga Amirka a daidai kuma lokacin da Rasha ke tsananta hare-hare ta sama a kasar.
Rundunar sojin Rasha dai ta ce mayakanta 63 ne suka mutu a wani harin rokoki da sojojin Ukraine suka kai wani ginin da ke dauke da dakarunta a gabashin yankin Donetsk.
Ba kasafai ba ne dai Rasha ke bayar da sanarwar mutuwar dakarunta a fagen yaki ba.
Ukraine ta ce ta kashe sojojin na Rasha akalla 400, bayan kuma ta kakkabo jirage marasa matuka 22 kirar Iran da sojojinta suka yi a 'yan kwanakin nan.
Mayakan gwamnatin Shugaba Vladimir Putin dai sun kaddamar da luguden wuta a yankunan Ukraine masu yawa, ciki har da Kyiv bbabban birnin kasar, inda ta lalata wasu cibiyoyin samar da wutar lantarki a birnin.