1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta ce za ta iya hada kai da Amirka

November 19, 2014

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce a shirye ya ke ya tattauna da Amirka harma ya bata hadin kai in har akwai mutunta juna a tsakaninsu.

Hoto: ALEXEI NIKOLSKY/AFP/Getty Images

Putin ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar sabon jakadan Amirka a Rasha John Tefft, inda ya ce a shirye ya ke ya baiwa Amirkan hadin kai in har za su mutunta muradun juna da kuma baiwa kowa 'yancinsa dama samun dai-dai to yadda ya kamata. Rasha dai ta shiga takaddama da kasashen yamma musamman Amirkan tun bayan da aka fara rikici a kasar Ukraine, inda kasashen na yamma ke zargin Rashan da iza wutar rikicin ta hanyar baiwa 'yan awaren gabashin kasar ta Ukraine da ke goyon bayan Moscow hadin kai da ma taimako.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe