1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta dakatar da cinikin Dala da kuma Yuro

June 13, 2024

Babbar kasuwar hannayen jari ta Rasha ta dakatar da cinikin kudaden dala da kuma yuro, sakamakon sabbin takunkuman da Amirka ta kakaba mata.

Rasha ta dakatar da cinikin Dala da kuma Yuro
Rasha ta dakatar da cinikin Dala da kuma YuroHoto: Yelena Afonina/TASS/dpa/picture alliance

Gwamnatin Washington ta sanar da cewa ta sanya takunkumi kan kasuwar hada-hadar kudaden kasashen waje na Rasha a matsayin sabuwar hanyar ladabtar da ita, sakamakon sabbin hare-hare da ta kai Ukraine.

Ana dai ganin cinikin kudaden kasashen waje shi ne babban madogar tattalin arzikin Rasha. Sakamakon faduwar darajar kudin kasar na rubles cikin shekaru 30 da suka gabata, tun bayan rushewar tsohuwar tarayyar Soviet, 'yan Rasha ke yin ajiyarsu da kudaden kasashen waje a lokacin matsin tattalin arziki.