1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Rasha ta dakile harin da Ukraine ta kai a birnin Moscow

Mouhamadou Awal Balarabe
August 21, 2024

Rundunar sojin saman kasar Rasha ta yi ikirarin harbo jiragen Ukraine marasa matuka guda 11 a lokacin da suka nufi Moscow da kewayen babban birnin kasar ba tare da samu asarar ko raunuka ba.

Irin jirgi maras matuki da Ukraine ta kai hari da shi a Moscow
Irin jirgi maras matuki da Ukraine ta kai hari da shi a MoscowHoto: Maksim Blinov/SNA/IMAGO

Magajin garin Moscow Sergei Sobyanin ya ce wannan na daya daga cikin manyan hare-hare da suka taba faruwa a birnin ta hanyar amfani da jirage marasa matuka. Sojojin na Ukraine sun tabbatar da kai hari kan na'urar kariya ta makami mai linzami samfurin S-300 da ke lardin Rostov a kudancin kasar Rasha.

Karin bayani:Shekaru 25 Putin na harkar mulki a Rasha 

Jagoran sojojin Ukraine ya ce da irin wannan makami ne Rasha ta yi amfani wajen kai hari kan gine-ginen fararen hula a Ukraine. Sai dai mataimakin shugaban kwamitin sulhu na kasar Rasha Dmitry Medvedev ya nunar da cewa, kasarsa ba za ta tattauna da Ukraine ba, bayan da fadar mulki ta Kiev ta mamaye lardin Kursk na kasar Rasha.